igo na Peoples Democratic Party (PDP), kuma a wanda zai tsaya takarar gwamanan Jihar Kaduna a shekaran 2019 - ASUPROM

Breaking

IDEAS AND INFORMATION

ADVERTISE WITH ASUPROM

Popular Posts

Sunday 23 July 2017

igo na Peoples Democratic Party (PDP), kuma a wanda zai tsaya takarar gwamanan Jihar Kaduna a shekaran 2019

Jigo na Peoples Democratic Party (PDP), kuma a wanda zai tsaya takarar gwamanan Jihar Kaduna a shekaran 2019, Alhaji Sani Suleiman, ya bukaci sabon shugaban jam'iyyar, Ahmed Makarfi da yin aiki tare da gwamnan Jihar Ekiti,, Ayo Fayose, tsohon ministan, Femi Fani- Kayode.

Lokacin da yake zantawa da manema labarai a headquater jami’yya na Abuja, Suleiman yace tsohon dan takaran gwamnan jihar Delta, Cif Sunny Onuesoke yana cikin wa’yanda Makarfi yakamata yayi aiki da su.

Yace ba zai iya misalta irin goyon bayan da Fani Kayode, Fayose, da Onuesoke su ka ba Makrfi lokacin rikicin jam’iyyar.

Rikicin PDP: Dole Makarfi yayi aiki da Fayose, Fani –Kayode-Suleiman
Rikicin PDP: Dole Makarfi yayi aiki da Fayose, Fani –Kayode-Suleiman
Suleiman yace “ Yanzu da jamiyyar ta shirya yin aikinta na samar da tsayayyar adawa da kuma rike matsayinta na babban jam’iyya a kasannan, muna bukatan wa’yannan gwarazan dimokradiyya dan ba da gudunmawar su wajen samar da cigaban jam’iyya da kuma samar da tsayayyar adawa ga mulkin APC.

KU KARANTA: Mamman Daura ne babban matsalan shugaba Buhari

“Lokacin da sanannun jigajigan jam’iyyar suka bar PDP, wasu suka boye, wasu kuma suka gudu zuwa kasashen waje saboda tsoron farautar siyasa daga APC, duk da haka wa’yannan basu ja da baya ba daga jam,iyyar PDP ba.

"Ina jajanta wa Gwamna Fayose na Ekiti, Nyesom Wike daga Rivers, Fani-Kayode da Onuesoke na Delta, wa’yanda suka kasance wakilan talakawa na gaskiya ".

No comments:

Post a Comment